BBC ta kammala barin ginin Bush House

Bush House
Image caption Bush House

Bayan shekuru saba'in (70), na watsa shirye shirye ga duniya daga ginin Bush House, a tsakiyar birnin London, yau BBC ta watsa labarun karshe daga dakunan watsa shirye shiryenta na Bush House din.

Mutane da dama ne suka yi cincirindo a kofar dakin watsa labarun, lokacin da mai karatanta labarun na karshe ya fito, bayan ya kammala labarun nasa, injiniyoyi kuma sun rufe na'urar yada labaran.

Sashen BBC mai watsa shirye shiryensa a harsuna daban daban ga duniya zai koma taki kadan zuwa sabon ginin watsa shirye shirye, da labarai na BBC.

Shi dai wannan gini ya ci zunzurutun kudi har dala biliyan guda da rabi don fadada ginin na Broadcasting House.

Tun a karshen watan da ya wuce ne sashen Hausa na BBC, da wasu sassan masu watsa shirye shirye ga kasashe cikin harsuna daban daban suka tare a sabon ginin.

Karin bayani