'Rayukan 'yan gudun hijira a Kenya na cikin hadari'

Dadaab Refugee Camp Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Hukumomin bayar da agaji dake aiki a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab a gabashin Kenya sun yi gargadin cewa dubun dubatar mutane na fuskantar barazana ga rayukansu saboda kudin da ake tallafa masu ya kusa karewa.

Hukumomin guda takwas ciki har da Oxfam da Save the Children sun ce ana bukatar karin dala million 25 cikin gaggawa don samar da sabbin matsugunai, da ruwan sha da kayan tsafta.

A cewar Christina Ruiz Manajar kula da aikin agaji ta kungiyar Christian Aid a Afirka abinda yawancin kungiyoyin agaji dake aiki a sansanin ke ji shine halinda ake ciki a sansanin yana munana, kuma ga shi kasashen duniya sun fara mantawa da sansanin.

A bara ne dai dubun dubatar 'yan gudun hijira suka kwarara zuwa cikin sansanin daga kasar Somaliya domin kauracewa fatara da kuma tashe-tashen hankullanda da kasar ke fama da su kari bisa ga fari mafi muni a cikin shekaru 60 da kasar ta fuskanta.

Karin bayani