Firayim Ministan kasar Mali ya ziyarci Nijar

Mayakan Ansar Deen a Mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mayakan Ansar Deen a Mali

Firayim Ministan kasar Mali, Cheick Modibbo Diarra ya kai wata ziyarar aiki Jamhuriyar Nijar ranar Alhamis, inda ya gana da shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Issoufou Mahamadou.

Sun tattauna a kan halin da kasar ta Mali ke ciki tun bayan da 'yan tawaye suka mamaye yankin arewacinta.

Haka kuma sun tattauna a kan hanyoyin da ake jin za su taimaka wajen kubutar da kasar ta Mali daga halin da take ciki, musamman yunkurin da kungiyr ECOWAS ke yi ta wannan fannin.

Kafin ya gana da hukumomin na Nijar dai praministan na Mali ya ziyarci wasu sojojin kasarsa da ke girke a kusa da Yamai, tun bayan da suka gudo daga yankin Kidal, sakamakon hare haren da 'yan tawaye suka kai musu.

Rahotanni daga Mali na cewa mayakan kungiyar kishin Islama ta Ansar-Deen a arewacin kasar ta Mali sun kora mayakan kungiyar 'yan aware ta Azbinawa daga yanki na karshe dake hannunsu.

An fatattaki mayakan Azbinawan ne daga garin Ansogo mai nisan kilomita dari daga garin Gao.

Karin bayani