Majalisar kasa ta Najeriya ta yi taro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A Najeriya yau ne majalisar kasa, wadda ta kunshi shugaban kasa da tsaffin shugabannin kasa da gwamnoni da kuma tsaffin shugabannin kotun kolin kasar, ta yi zamanta a Abuja.

Sai dai ukku ne kawai daga cikin tsoffin shugabannin kasar bakwai suka halarci taron.

Ba a dai bayar da wani bayani a karshen taron ga manema labarai ba.

Sai dai bincike ya nuna cewa batun inganta sha'anin tsaro ne tattaunawar ta fi maida hankali a kai.

Karin bayani