Mutane kusan dari sun mutu a gobarar tankar mai

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Ba wannan ba ne karo na farko da mutane ke mutuwa sakamakon konewar tankar mai a Najeriya

Rahotanni daga Jihar Rivers a kudu maso kudancin Najeriya sun kiyasta cewa mutane kusan dari sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka kone bayan da wata motar tankar mai ta fadi.

Mutanen dai na kokari ne na kwasar man da ke zuba daga tankar da ta yi hadari a garin Ahoada sai ta kama da wuta.

'Yan sandan jihar ta Rivers sun tabbatar da faruwar al'amarin, ko da yake ba su bayar da takamaiman adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba.

Ba wannan ba ne karo na farko da mutane suka rasa rayukansu a Najeriya ta hanyar tashin wuta yayin da suke yunkurin kwasar mai ko dai daga tankar da ta yi hadari ko kuma a bututan man da suka fashe.