Tankar mai ta kashe mutane da dama a Najeriya

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Ba wannan ba ne karo na farko da mutane ke mutuwa sakamakon konewar tankar mai a Najeriya

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta tabbatar da cewa ta gano gawarwakin mutane casa'in da biyar yayainda wasu mutanen goma sha takwas ke kwance a asibiti sakamakon kama wutar da wata tankar mai ta yi yayin da mutanen kauyen Okobe a Jihar Rivers ke kokarin kwasar mai.

Hukumar ta NEMA ta kuma bayyana cewa al'amarin ya kuma shafi kananan motoci guda biyu.

Motar tankar dai ta yi hadari ne a kauyen na Okobe da ke karamar hukumar Ahoada.

Rahotanni sun ce jami'an 'yan sanda, da na 'yan kwana-kwana, da na NEMA na cikin ma'aikatan da ke yunkurin ceto wadanda al'amarin ya rutsa da su.

Ba wannan ba ne karo na farko da mutane suka rasa rayukansu a Najeriya ta hnayar tashin wuta yayin da suke yunkurin kwasar mai ko dai daga tankar da ta yi hadari ko kuma a bututan man da suka fashe.