An binne mamatan gobarar mai a Najeriya a kabari daya

Nigeria tanker
Image caption Motar tankar da ta yi hadari a Jahar Rivers

An yiwa mutane 85 daga cikin wadanda suka mutu a gobarar tankar man da ta afku jiya a Jahar Rivers ta Najeriya jana'iza ta bai daya.

Rahotanni sun ce an kuma mika gawawwakin wasu mutane shida da aka shaida ga 'yan uwansu.

Bayan haka ne mahukumtan jahar suka yanke shawarar binne dukkanin sauran mamatan wadanda dukkansu sun kone ta yadda ba a iya gane su acikin rami daya.

Wakilin BBC a yankin na Niger Delta Abdul Mohammed Isa wanda ya isa wajen kafin fara binnewar yace abin ba ya da kyan gani:'' ...a kusa dani nan kuma ga wani rami cike da gawawwaki dukkansu sun kone wasu ma har kwakwalwarsu ta fito,wasu kwarangwal ne kawai ya rage nasu wasu kuma da hanjinsu duk sun fito.''inji shi.

Sanadi

Gobarar dai ta tashi ne a lokacinda mutanen ke kokarin kwasar man da ke zuba daga wata tankar da ta yi hadari a garin Ahoada dake jahar ta Rivers.

'Yan sandan jihar ta Rivers sun tabbatar da faruwar al'amarin, ko da yake ba su iya bayar da takamaiman adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba.

An dai jin daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu har da masu wucewa ta kusa da wurin kan motoci da kuma babura.

Wannan dai bashi ne karo na farko da mutane suka rasa rayukansu a Najeriya ba ta hanyar tashin wuta yayin da suke yunkurin kwasar mai ko dai daga tankar da ta yi hadari ko kuma a bututan man da suka fashe.

Karin bayani