Shugabannin Afrika sun tattauna a Habasha kan kasar Mali

au Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron kasashen Afrika wato AU

Shugabannin kasashen Afirka da ke taro a Habasha sun ce rikicin da ake fama da shi a Mali wani babban kalubale da ke fuskantar nahiyar.

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast ya shaidawa taron, wanda ake gudanarwa a Addis Ababa, baban birnin kasar ta Habasha, cewa kungiyoyin 'yan ta'adda suna kokarin samawa kansu mafaka a Mali.

Ya kuma ce yanayin kasar ta Mali na barazana ga zaman lafiya da tsaron daukacin yankin.

Tun a farko-farkon bana ne dai gamayyar masu tsatstsauran ra'yin Islama da 'yan tawaye suka kwace iko da artewacin Mali bayan juyin mulkin da ya kifar da zababbiyar gwamnatin kasar.

Karin bayani