Hillary Clinton ta gana da Shugaba Mursi a birnin Alkahira

mursi clinton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammed Mursi da Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta sauka a Masar don tattaunawa da sabon shugaban kasar, Mohammed Mursi.

Misis Clinton ta jaddada goyon bayan Amurka ga shirin kasar Masar na komawa turbar dimokuradiyya.

Wakilin BBC ya ce wannan ganawa ce da shekaru biyu da suka wuce ba wanda zai taba tunanin za ta faru. A farkon zamansu Clinton ta yi tsokaci kan yadda sauye-sauye a kasar ke jan kafa, yayinda Mursi kuma ya ce ya yi farin ciki da zuwanta.

Hillary Clinton kuma jaddada bukatar Masar ta mutunta yarjejeniyoyinta na kasa da kasa musamman na zaman lafiya da Isra'ila.

Misis Clinton ta kuma bukaci Shugaba Mursi ya cika alkawuran daya dauka na kare 'yancin tsiraru da kuma mata.

Za ta kuma gana da kungiyoyin farar hula da jagoran majalisar sojin da ta karbi mulki bayan kifar da Shugaba Hosni Mubarak bara.

Karin bayani