Ana ci gaba da kada kuri'a a zaben Jihar Edo

Wasu 'yan Najeriya suna kada kuri'a Hakkin mallakar hoto b
Image caption Wadansu 'yan Najeriya suna kada kuri'a a zaben kasa da ya gabata

A Najeriya, ana can ana ci gaba da kada kuri'a a zaben gwamna a Jihar Edo da ke kudu maso kudancin kasar, inda jam'iyyun siyasa bakwai suke takara, kuma mutane kimanin miliyan daya da dubu dari shida suke kada kuri'a.

Rahotanni dai sun ce an fara aikin zaben a kan lokaci kamar yadda aka tsara a galibin rumfunan zabe, sai dai kuma duk da haka akwai 'yan matsalolin da ba a rasa ba.

Wani mazauni Benin, babban birnin jihar, Abubakar Osatoameh, ya shaidawa wakilin BBC, AbdusSalam Ibrahim, cewa ko da yake mutane sun fito yadda ya kamata, wadansu sun kauracewa rumfunan zaben.

“Yawancin mutane suna [ganin] kamar yau za a yi fada; [shi] ya sa wasu ma ba su fara fitowa ba”, inji Osatoameh.

Ya kuma kara da cewa “Ko yanzu ma wadanda suka kira ni sun kai kusan talatin, na kuma ce musu su zo ba wani fada”.

A wadansu wurare kuma an yi kukan rashin isar kayan zabe a kan lokaci, al’amarin da Hukumar Zabe ta danganta da rashin jami’an tsaron da za su yiwa kayan zaben rakiya.