Ana gudanarda zaben gwamna a jahar Edo ta Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yadda ake kidayar kuri'u a zaben Najeriya.

An bude runfunan zaben gwamna a jihar Edo dake kudancin Najeriya domin zabar sabon gwamna sakamakon karatowar karshen wa'adin farko na gwamnan jahar mai ci yanzu.

'Yan takarar jam'iyyun siyasa bakwai ne dai ke fafatawa a zaben na yau assabar, ciki kuwa har da gwamnan jihar da ke kan mulki Comrade Adams Oshiomole.

Wakilin BBC dake jahar Abdussalam Ibrahim Ahmed yace tun da safe masu zabe suka fara isa runfunan zaben inda ake tsammanin masu zaben fiye da miliyan daya da rabi su jefa kuriarsu.

Wannan zaben dai yana jan jama'ar kasar da yawa, saboda yadda a kowacce daga cikin jam;iyyun ACN mai mulkin jahar da PDP mai mulkin kasar ke kokarin ganin ta samu nasara.

Karin bayani