An fara Babban Taron Tarayyar Afirka a Habasha

Babban taron Tarayyar Afirka
Image caption Mahalarta babban taron Tarayyar Afirka

An bude Babban Taron Tarayyar Afirka na wata shida-shida a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Ana sa ran wani sabon yunkurin warware kiki-kakar shugabancin hukumar gudanarwar kungiyar ne zai kankane ajandar taron.

Yayin taron kungiyar da aka gudanar a watan Janairu, ba wanda ya samu isasshen goyon bayan da ake bukata a cikin mutane biyun da ke takara—Nkosazana Dlamini-Zuma ta Afirka ta Kudu da Jean Ping, shugaban hukumar mai ci.

Masu aiko da rahotanni sun ce a wadansu lokutan, zazzafar takara kan dauke hankali daga kan matsalolin tsaron da ke damun wadansu sassan nahiyar, musamman rikicn Mali da takaddamar Sudan da Sudan ta Kudu.

Yayin taron dai, shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu sun gana a karo na farko tun bayan da kasashen suka kusa gwabza yaki a farkon wannan shekarar.

Bayan ganawar ce kuma Omar al-Bashir da Salva Kiir suka yi musafaha.

Gidan rediyon kasar Sudan ya bayar da rahoton cewa shugabannin biyu sun bayyana kyakkyawan fatan cewa danganatakar da ke tsakanin kasashen nasu za ta inganta.

Sai dai kuma sun yi sabani a kan shata iyakoki, da biyan kudin safarar man fetur, da kuma karkasa bashin da ake bin kasashen.