Hillary Clinton ta gana da shugaban sojin Masar

Hillary Clinton da Hussein Tantawi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakatariyar Harkon Wajen Amurka, Hillary Clinton da shugaban majalisar sojin Masar, Hussein Tantawi

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta tattauna da manyan jami'an sojin Masar, sa'o'i bayan ta bukace su su tabbatar da cewa kasar ta koma kan kammalalliyar turbar dimokuradiyya.

An bayar da rahoton cewa Misis Clinton ta yi wata ganawa ta tsawon fiye da sa'a guda da Field Marshal Hussein Tantawi, mutumin da ke jagoranatar majalisar sojin da ta karbi mulki bayan kawar da Shugaba Mubarak bara.

Wakiliyar BBC a Alkahira ta ce yayin ganawar, Misis Clinton ta jaddada sakon da ta mika jiya yayin wani taron manema labarai, inda ta yi kira ga sojoji su koma matsayinsu na tsaron kasa su sarayar da ikon da suke ta kokarin kankamewa a 'yan watannin da suka gabata.

Ranar Asabar Misis Clinton ta gana da magajin Mubarak, Muhammad Mursi; ta kuma bukace shi da ya yi aiki tare da sojojin, tana mai cewa a halin da ake a Masar ana bukatar cude-ni-in-cude-ka.

Karin bayani