Za a kafa rundunar soji a kan iyakar Rwanda da Congo

au Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun kungiyar tarrayar Afrika

Rahotanni daga wurin taron kolin shugabannin kasashen tarayyar Afirka sun ce shugabannnin kasashen Rwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun amince da kafa wata rundunar soji ta kasa-da-kasa, da za ta yi aiki a kan iyakokinsu don kawar da mayakan sa-kai daban daban da ke gabashin Congo.

Tun da farko shugabannin biyu, Paul Kagame da Joseph Kabila, sun yi wata tattaunawa ta gaba-da-gaba wadda ba su saba yin irinta ba a wurin taron kolin.

Nausawar da 'yan tawaye ke yi kwanan nan a gabashin Congo ta tilastawa mutane da dama tserewa dga gidajensu.

Gwamnatin kasar ta Congo dai tana zargin Rwanda da taimakawa 'yan tawayen, amma gwamnatin Rwandan ta musanta hakan.

'Matsalar Shugabanci'

An samu rarrabuwar kawuna a tsakanin shugabannin kasashen Tarayyar Afirka wadanda ke halartar babban taron dangane da wanda ya kamata su goyawa baya a cikin 'yan takarar shugabancin hukumar kungiyar.

Mutane biyun da ke fafatawa dai, wato Nkosazana Dlamini-Zuma ta Afirka ta Kudu da Jean Ping na Gabon sun sake tsayawa takara ne duk da cewa sun kasa samun goyon bayan da ake bukata a watan Janairu.

Sai dai kuma Dlamini-Zuma ta ce ba ta ga dalilin da zai sa zaben ya kawo rarrabuwar kawuna ba.

Ta ce "ba na tunanin kan nahiyar zai rabu saboda zaben, duk wanda aka zaba zai tabbatar da cewa ya yi aiki tare da kowa, ba tare da yin la'akari da inda suka fito da wanda suka zaba ba".

Karin bayani