An kara daurawa mata 250 a jihar Kano

kano
Image caption Kayan daki da gwamnatin jihar Kano ta baiwa amaren

A jihar Kano dake arewacin Najeriya an daurawa mata 250 aure da mazajensu a wani bangare na shirin aurar da mata dubu daya da hukumar Hizba ta kuduri aniyar yi a jihar.

'Yan mata uku uku da kuma zaurawa biyu biyu aka zabo daga kananan hukumomin jihar 44 aka kuma daura musu auren da mazajen da suka daidaita da su.

Gwamanatin jihar ta baiwa amaren kayan daki da kuma kudin da za su yi jari, yayin da aka kuma samu gudunmuwa da dama daga wasu bangarorin.

A watan Mayun bana ma dai an daurawa wasu matan dari aure a zagaye na farko na shirin.

Karin bayani