Yan Najeriya 327 ne suka dawo daga Libya

Image caption Najeriya

Kimanin 'Yan Najeriya dari uku da ashirin da bakwai ne suka dawo gida daga Kasar Libya a karshen makon da ake ciki.

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya wato NEMA ita ce ta tarbi 'yan Najeriyar a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammad dake lagos.

Ko a watan Maris din da ya gabata hukumar ta NEMA tare da hadin gwiwar kungiyar lura da masu yawan cirani ta duniya wato IOM sun kwaso kimanin 'yan Najeriya dari tara da casa'in da daya daga Kasashen Masar da Tunisia a lokacin da guguwar siyasa ke kadawa a yankin Arewacin Afirka.

NEMA tace ya zuwa yanzu 'yan Najeriya dubu uku ne suka dawo daga Kasar Libyan.

Wannan lamari dai na zuwa ne tun bayan juyin juya halin da aka samu a kasar, wanda kuma yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin marigayi Kanal Mu'ammar Gaddafi.

Karin bayani