Hillary Clinton zata gana da sojin Masar

Clinton Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hillary Clinton a Masar

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton na cigaba da ziyararta a Masar, inda a yau Lahadi za ta gana da shugabannin soji.

A ranar Asabar Mrs. Clinton ta gana da zababben shugaban kasar na Masar na farko Muhammad Mursi na kungiyar 'yan uwa Musulmi, inda ta bukace shi ya yi aiki da shugabannin sojin domin tabbatar da mika mulki ga farar hula.

Mrs. Clinton ta ce akwai bukatar hadin kai tsakanin sojojin da kuma gwamnatin farar hula.

Wakilin BBC a Alkahira yace mai yiwuwa ne Amurka na son sojojin su sa ido ne kan gwamnatin ta masu kishin Islama.

Karin bayani