Ana zargin Syria da kai harin Tremseh

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani da yaji rauni a Tremseh

Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya sun ce da alamu harin da gwamnatin kasar ta kai ranar Alhamis a kauyen Tremseh ya nufaci gudaddun soji ne da 'yan adawa masu fafutuka.

Tawagar majalisar dinkin duniyar ta ce dakarun gwamnati sun yi amfani da muggan makamai lokacin kai harin.

Yan adawa na cewa kisan kiyashi a ka yi agarin, inda aka hallaka fiye da mutane dari biyu, sai dai ba su bada wata kwakkwarar shaidar da ta nuna hakan ba.

Gwamnatin Syria kuwa na cewa tana kai hari ne kan abinda ta kira shekar 'yan ta'adda ko kuma inda 'yan tawaye ke fakewa.

Karin bayani