An gwabza kazamin fada a kewayen Damascus

tremsa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin da aka kai a kauyen Tremsa

An bayar da rahotonnin gwabza kazamin fada a kewayen babban birnin Syria, wato Damascus.

A cewar masu fafutuka, sojojin gwamnati sun yi amfani da tankokin yaki da makaman atilare a fafatawar da suka yi da mayakan 'yan tawaye na Free Syrian Army.

Tashin hankalin na baya-bayan nan dai ya auku ne a gefen birnin, a yankunan da suka hada da Tadhamun, da Midan, da kuma sansanonin da ke kusa na Falasdinawa 'yan gudun hijira.

An bayar da rahoton cewa mazauna yankunan sun tsere daga gidajensu.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta yi amanna rikicin na Syria ya zama yakin basasa.

Kungiyar dai ta ce a yanzu tana dauka cewa rikicin da ake fama da shi a daukacin kasar ta Syria ya fada karkashin tanade-tanaden Yarjejeniyar Geneva, wato Geneva Convention, wacce ta shata ka'idojin yaki.

A baya dai wurare uku ne kawai a kasar ta Syria suka fada cikin wannan aji.

Kungiyar ta Red Cross ta ce Yarjejeniyar ta Geneva ta baiwa bangarorin da suke yaki dama su yi amfani da karfi daidai gwargwado, amma kuma ta tanadi hukunce-hukuncen aikata laifukan yaki.

Karin bayani