AU ta zabi mace ta farko a shugabanci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jean Ping da Dlamini-zuma

Kungiyar kasashen Afrika ta zabi Nkosazana Dlamini-Zuma ta Afrika ta kudu a matsayin sabuwar shugabar hukumar zartarwar kungiyar.

Ita ce dai mace ta farko da ta dare wannan mukami.

Ms Dlamini-Zuma ta kada Jean Ping na Gabon wanda ke shugabantar hukumar zartarwar kungiyar tun shekarar dubu biyu da takwas.

Sabuwar shugabar tace za ta mai da hankali ne kan yi wa kungiyar garambawul.

Wakilin BBC yace manazarta na ganin dauki-ba-dadin da aka sha a zaben ta ya jawo rarrabuwar kai a Nahiyar Afrika; kuma sai ta yi aiki wurjan-jan kafin ta cimma manufarta.

Karin bayani