Kofi Annan zai gana da Lavrov a Moscow

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kofi Annan

Wakilin majalisar dinkin duniya na musamman akan rikicin Syria, Kofi Annan zai isa Moscow idan an jima a yau Litinin domin tattaunawa da ministan harkokin waje na Rasha Sergei Lavrov.

Rasha dai na da kwakkwarar alaka da gwamnatin Syria, kuma ana ganin taimakon da Rasha ke baiwa shugaba Assad ne ya taimaka masa cigaba da rike ragamar mulki.

Sau tari, Rasha na hawa kujerar na-ki a majalisar dinkin duniya game da batun baiwa dakarun kasashen waje izinin kutsa kai cikin Syria.

Ana jin cewa Mr. Annan zai bukaci Mr. Lavrov ne da ya matsawa mahukuntan Syria su dauki matakan barin mulki.

Karin bayani