BBC navigation

Rasha ta soki kasashen yamma

An sabunta: 16 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 15:18 GMT

Sergei Lavrov, ministan harkokin waje na Rasha

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce kokarin shafawa kasarsa kashin kaji ne, yunkurin da kasashen yammcin duniya ke yi na sa Rasha ta amince a tattauna yuwuwar daura takunkumi a kan Syria a majalisar dinkin duniya.

A lokacin wani taron manema labarai , Mr Lavrov ya ce matsayin Rasha a rikicin kasar ta Syria bai sauya ba.

Mista Lavrov ya ce, Rasha ba ta goyon bayan kowanne bangare a rikicin Syria, kuma yace, manufarmu ita ce kada mu bari a janyo rudani a kasar Syria, ta yadda zata fada hadarin wargajewa, kada kuma hakan ya kara dagula al'amurra a yankin baki daya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.