Yobe: ana harbe-harben bindiga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Damaturu a watannin baya

Rahotanni daga Damaturu babban birnin jahar Yobe a arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a tsakiyar birnin.

Wasu mazauna birnin dai sun ce tun daga misalin karfe daya na rana ne suka fara jin karar harbe harbe, a kusa da ofishin SSS da na JTF dake wajen.

Wani mazauna garin na Damaturu sun ce, lamarin ya taba wani bangare na ofishin JTF daga tsakiyar birnin.

Cikin 'yan watannin nan dai garin Damaturu ya sha fama da harin da ake dangantawa ga kungiyar Boko Haram.