Clinton ta ce gwamnatin Syria ta kusa rushewa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hillary Clinton

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka Hillary Clinton ta ce al'amuran da ke faruwa a Syria, wadanda suka hada da sauya shekar manyan jami'ai da kuma tsanantar yaki a birnin Damascus, alamu ne da ke nuna gwamnatin kasar ba za ta yi nisan kwana ba.

Tace gaba dayan mu mun san lokacin kawai ake jira.

Ta kara da cewa abin takaici ne kasashen duniya sun kasa hada kai su yi magana da murya guda a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya game da batun Syria.

Kasar Rasha dai ita ce kan gaba wajan hawa kujerar naki a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan Syria, abin da ya ke nuni da kwakkwarar alakar dake tsakanin gwamnatin Syriar da kuma ta Rasha.

Karin bayani