An sake cilla roka a garin Bukur na Jihar Filato

Taswirar Najeriya mai nuna Jihar Filato
Image caption Taswirar Najeriya mai nuna Jihar Filato

Rahotanni daga Jihar Filato a Najeriya sun ce an sake harba wadansu makaman roka a garin Bukur da yammacin ranar Talata, bayan wanda aka harba da safiyar ranar a wata makaranta—wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro dan shekara goma.

An kuma bada labarin harbe-harben bindigogi bayan cilla makaman na roka.

Wani mazaunin garin ya bayayana cewa mutane na yunkurin kamala saye-sayensu su hanzarta zuwa gidan fara doka hana fita ne sai kwatsam aka sake harba rokokin har guda uku.

Sai dai kuma a cewarsa, ba wanda ya rasa ransa a harin.

Kakakin Rundunar Tsaro ta Musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a Jihar ta Filato, Kyaftin Salisu Mustapha, ya shaidawa wakilin BBC Is’haq Khalid cewa yana da labarin cilla makaman amma bai samu cikakken bayani.

Sai dai kuma, a cewarsa, jami’ansu na wurin.

A hari na farko da aka kai da safiyar ranar dai jami’an tsaro a jihar sun ce an auna makarantar Nurul Islam ce, amma dai gurnetin bai sami makarantar ba—amma dai ya ragargaza wani yaro dan kimanin shekaru goma kana ya lalata ginin wani gida dake dab da makaranatar.

A baya ma an kama wadansu mutane biyu ana zargin suna kokarin dasa bam a kewayen makarantar, baya ga wani bam da hukumomi suka kwance kwanakin baya a yankin.

Rahotonnani dai sun nuna cewa al’amarin ya haifar da kisan dauki daidai a wadansu sassa na birnin Jos da Bukur inda ake yawan fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini; wadansu bayanai ma sun ce mutane akalla uku sun rasa rayukansu wadansu kuma sun jikkata.

Jama’a da dama da masu lura da al’amura dai cewa suke yi akwai bukatar hukumomin tsaro su kara tsaurara bincke a yankin domin gano irirn wadannan makamai, wadanda sau da yawa akan yi yake-yaken kasa da kasa da su.