An ci kamfanin Shell tara

Image caption Rijiyar mai

Gwamnatin Najeriya ta ci kamfanin mai na Shell tarar dala biliyan biyar saboda malalar mai a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Malalar man ta auku ne a yankin hakar mai na Bonga cikin watan Disambar da ya gabata, kuma lamarin ya haddasa malalar gangar mai dubu arba'in cikin teku.

Sai dai kuma wani kakakin kamfanin na Shell ya maida martani yana mai cewa, tarar da aka ci kamfanin ba ta halasta ba tunda an dau dukkan matakan da suka kamata domin hana lamarin yin wata illa ga muhalli.

Mazauna yankin Niger Delta sun sha yin korafi akan yadda suka ce, hakar mai na yin illa ga muhallinsu.l