Safarar makamai na iza wuta a Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption shugabar kasar Liberia, Sirleaf

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta ce fataucin miyagun kwayoyi, da safarar makamai ne ke kara iza wutar tada kayar baya a Nahiyar Afrika.

Mrs Sirleaf ta shaidawa BBC cewa karuwar kungiyoyin 'yan bindiga irinsu Boko Haram a Najeriya, da Ash-Shabab a somalia, da kuma Ansarud Din a Mali abin takaici ne kwarai.

Tace Liberia za ta shige gaba wurin ganin an rattaba hannu kan yarjejeniyar takaita yaduwar kananan makamai kasancewar babu wata kasar Afrika da ke sana'anta makaman sai dai ta shigo da su daga ketare.

Ana zargin yawaitar makamai a hannun fararan hula a Nahiyar.

Karin bayani