Iraqi za ta gurfanar da tsohon Jakadan syria a kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nawaf Fares

Kasar Iraqi ta ce zata bi kadun sharia kan Jakadan Syria a Baghdad wanda ya bujerewa gwamnatin Syrian makwon da ya gabata.

Mai bada shawara ga Prime Minsitan Iraqi Nouri Almaliki ya ce jawaban da Nawaf Fares yayi ga kafafan yada labarai ya fasa kwai ne kan hadin gwiwar kai hari da akayi a Iraqi shekaru da dama da suka wuce.

Kamar wasu da dama manyan mutane da suka bar gwamnatin Syria, Nawaf fares na da wasu labarai da zai bayyana kan gwamnatin Syria tsohuwar uwar gijiyarsa.

Ya shaidawa wata Jarida Sunday telegraph cewa bayanda Amurka ta mamaye Iraqi a shekarar ta dubu biyu da uku, Syria ta yi hadin gwiwa da yan Alqaeda don tarwatsa dakarun sojin Amurka.

Ya ce shi da kansa ya taimakawa gwamnatin Damascus ya aika da wata tawaga ta masu Jihadi zuwa kasar ta Iraqi wanda su ne suka kai hari a cikin Syria. Ya ce yawancin asarar da harin ya jawo a Syria shugabannin kasar ne suka bada umarnin yin hakan.

Karin bayani