Isra'ila za ta yi Jami'a a Yammacin Kogin Jordan

Image caption Israila

Mahukuntan Isra'ila sun amince da wani mataki mai cike da rudani na samar da jami'a ta farko a gabar Yammacin Kogin Jordan.

Mahukuntan sun amince da daga darajar wata kwaleji ce da ke unguwar Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ta Ariel bisa shawarar Ministan ilimi na Isra'ila.

Su dai 'yan kama-wuri-zauna na kallon wannan mataki a matsayin wata gagarumar nasara yayinda Palasdinawa da malaman jami'o'in Isra'ila suka soki lamarin.

Wakiliyar BBC ta ce dokokin kasa da kasa sun haramta kama-wuri-zauna kodayake Isra'ila na musanta hakan.

Palasdinawa na ganin kirkirar jami'ar tamkar manuniya ce cewar Isra'ila ba ta shirya barin gabar yammacin kogin Jordan ba, wadda Palesdinawan ke fatan ganin ta fada karkashin ikon kasar da za su kafa a nan gaba.

Karin bayani