An bayyana sakamakon zaben majalisa a Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zabe a Libya

Gamayyar jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi, ta samu rinjaye a zaben majalisar dokokin Libya na farko da aka gudanar bisa tafarkin dimokradiyya a cikin shekaru da dama.

Kawancen National Forces Alliance karkashin jagorancin Mahamoud Jibril, wanda ya rike mukamin Piraministan rikon kwarya bayan hambarar da gwamnatin kanar Ghaddafi ta lashe talatin da tara daga cikin kujeru tamanin da jam'iyyun siyasa suka yi takara.

Jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ce ta zo ta biyu da kujeru goma sha bakwai.

Wakiliyar BBC tace sabuwar majalisar na da ikon kafa dokoki, kuma ita ce ke da hakkin samar da sabuwar gwamnatin rikon kwarya tare da fitar da sabon tsarin mulkin kasar.

Karin bayani