An halaka jami'an gwamnatin Syria su uku

Janar Hassan Turkomani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daya daga cikin jami'an da aka kashe, Janar Hassan Turkomani

Gidan talabijin na Syria ya bayar da rahoton halaka wadansu manyan kusoshin gwamnatin Shugaba Assad su uku a wani harin kunar bakin wake a Damascus, babban birnin kasar.

Surukin shugaban kasar, Assef Shawkat, na cikin wadanda aka kashe.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan tsaro a kasar.

A cewar gidan talabijin din, shi ma Ministan Tsaron kasar Daoud Rajiha, ya rasa ransa a harin.

Haka nan kuma an halaka Janar Hassan Turkmani, wanda ke jagorantar taron da ake gudanarwa a lokacin da aka kai harin.

Sojojin kasar ta Syria da suka sauya sheka zuwa bangaren 'yan tawaye sun ce su ne ke da alhakin kai harin.

Amma dai gwamnatin kasar ta ce a yanzu ma za ta kara matsa kaimi ne fiye da baya wajen kai farmaki a kan wadanda ta kira 'yan ta'adda wadanda Amurka da Isra'ila ke marawa baya.

Ministan Yada Labaran kasar, Omran Zoabi, ya ce “Harin bam din da sauran abubuwan dake faruwa a Syria aikata kisan kai ne, da zagon kasa da kisan gilla da kuma hare-haren bam”.

Ministan ya kuma musanta rahotannin cewa an kai hari a kan hedkwatar rundunar soja ta hudu, wadda ke gadin fadar shugaban kasar.

Wani kakakin fadar White House ya ce da wannan harin iko ne ke neman subuce wa Shugaba Bashar al-Assad.

Furucin nasa ya zo kusan daya da na Sakataren Tsaron kasar ta Amurka, Leon Pannetta, wanda tun farko yake cewa tashin hankalin da ake yi a Syria na neman wuce makadi da rawa.

A halin da ake ciki, wakilin Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya ce an dage kada kuri'a a kan matakan da za a dauka kan gwamnatin Syriar zuwa ranar Alhamis.

Wakilin musamman na kasashen duniya a rikicin kasar ta Syria, Mr Kofi Annan ne ya nemi a dan jinkirta.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya la'anci harin kunar bakin waken da yayi sanadiyar mutuwar manyan jami'an Syriar biyu.

Hague ya ce "Hare-haren sun kara tabbatar da bukatar da ake da ita ta samun wani kuduri mai karfi na Majalisar Dinkin Duniya da zai kawo karshen rikicin kasar ta Syria cikin gaggawa".

Kafin haka Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya , Ban-Ki Moon ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki mataki na bai daya kan rikicin Syriar, bayan wata ganawa da shugaban China, Hu Jintao, a birnin Beijing.

Karin bayani