Gwamnatin Assad na hanyar rushewa, in ji Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barack Obama

Amurka ta ce kisan da aka yi wa manyan jami'an gwamnatin Syria a harin bom na ranar Laraba ya nuna cewa madafun iko na kubuce wa Shugaba Bashar al-Assad.

Fadar gwamnatin Amurka, White House, ta ce Barack Obama ya tattauna ta wayar tarho da Shugaba Vladamir Putin na Russia game da karuwar tashin hankali a Syria.

A cewar sanarwa da fadar ta fitar, shugabannin biyu sun nuna damuwarsu dangane da tashin hankalin na Syria, inda suka amince su goyi bayan samun sauyin gwamnati nan ba da dadewa.

Sanarwar ta kara da cewa shugabannin sun ce hakan ne zai kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Syria.

Sai dai fadar Kremlin ta Russia ta ce har yanzu akwai bambance-bambance tsakaninta da manyan kasashen duniya dangane da yadda za a bullowa rikicin kasarta Syria.

Kakakin gwamnatin Russia, Dmitry Peskov, ya ce shugaba Obama ne ya bukaci tattaunawar da suka yi da Vladimir Putin, inda ya kara da cewa duk da yake shugabannin sun amince a tsagaita wuta a rikicin na Syria, sai dai har yanzu suna da mabambantan hanyoyin da suke gani za a bi don shawo kan rikicin Syria.

Hukumomin Syria sun ce mutanen da aka kashe sun hada da Assef Shawkat, wani surukin Mista Assad da Ministan tsaron kasar, Daud Rajha.

Kungiyar 'yan tawaye ta Free Syrian Army ta ce ita ce ta dana bam din.

Shugaban kungiyar 'yan tawayen Syrian National Council, Abdul-Basid Seida, ya ce lokaci kankane ya rage wa gwamnatin Shugaba Assad ta ruguje.

Ita dai Syria ta zargi Amurka da Israela da yin amfani da wadanda ta kira 'yan ta'adda don kai wa jami'an gwamnatinta harin da ya yi sanadiyar mutuwarsu.

Karin bayani