China zata taimakawa kasashen Afirka

Taron China da Afirka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taron China da Afirka

Shugaba Hu Jintao na China ya yiwa Gwamnatocin Afrika alkawarin bashin dola biliyan 20 a cikin shekaru uku.

Ya ce bashin zai taimaka wajen samar da ababan more rayuwa irin su hanyoyi da aikin gona da kuma bunkasa kasuwanci.

Shugaba Hu na yiwa Shugabannin Afrikan jawabi ne a farkon taron hadin kan China da Afrika wanda aka bude a yau a birnin Beijing.

Babban makasudin taron dai shi ne duba yadda za a kara kyautata huldar ciniki da kasuwanci tsakanin kasashen na Afrika da kasar China musamman ma gajiyar da nahiyar ka iya samu daga alakarta da kasar ta China.

A cikin yan shekarun nan dai China ta kasance babbar abokiyar huldar kasuwanci da kuma tushen saka jari ga Afrika, yayin da ta ke neman kayan sarrafawa don zaburadda tattalin arzikinta dake bunkasa.

Shugaban kasar Nijar, Mahammadou Issoufou, na cikin shugabannin Afrika da ke halartar taron

Karin bayani