An fara azumin watan Ramalana

Image caption Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar

A ranar Juma'a ne al'ummar musulmi a sassa daban-daban na duniya suka fara azumin watan ramalana.

A Najeriya, a ranar Alhamis da dare ne mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya sanar da ganin sabon watan ramalana a jihohi takwas na kasar.

Jihohin sun hada da Gombe, da Kebbi, da Katsina, da Zamfara, da Kaduna, da Yobe, da Niger da kuma Sokoto.

Azumin watan ramalana dai na daya da cikin shika-shikan musulunci.

Ana kwashe kwanaki ashirin da tara ko talatin ana yin azumin.

Uztaz Hussaini Zakariyya, wani malami addinin musulunci da ke Abuja, ya shaida wa BBC cewa ana so musulmi su zage-dantse wajen bautar Allah a watan.

Ya kara da cewa ana rubanya lada ga duk mutumin da ya gabatar da ayyukan alheri a cikin watan.

Karin bayani