Ana ci gaba da juyayin kisan mutane a Colorado

Dan bindiga ya harbe mutane a Sinima Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan bindiga ya harbe mutane a Sinima

Shugaba Obama da abokin hammayarsa Mitt Romney, sun dakatar da yakin neman zaben da suke yi saboda kashe mutannen da aka yi a wata sinima a jihar Colorado.

Mista Obama ya ce ya kadu matuka kuma abin bakin ciki ne, kashe mutane 12 da aka yi tare da raunata wasu 59 a sinima din.

Inda ya ce "za mu dauki matakan da suka dace don kare duka al'ummarmu.

Muna tare da makwabtanmu na Colorado a wannan lokaci mai wuyar gaske.

Shi kuma Mista Romney cewa yayi, jama'a suyiwa mamatan addu'a.

Karin bayani