Gobarar jirgin ruwa ta hallaka mutane 15 a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Najeriya ta yi iyaka da tekun Atlantika daga kudu

Akalla mutane goma sha biyar ne suka mutu bayan da wata gobara ta tashi a cikin wani jirgin ruwan dakon danyen mai a Jihar Rivers dake kudancin Najeriya.

Haka ma wadansu mutanen biyar na jinya a asibiti sakamakon raunukan da suka samu a hadarin wanda ya auku da safiyar ranar Jumu'a.

Rahotanni sun ce ma'aikatan kashe gobara na can suna kokarin ganin sun shawo kan wutar wadda ta tashi a cikin Tekun Atlantika.

Wata gobara da ta tashi bayan da wata tankar mai ta yi hadari a jihar a makon jiya ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari daya.

Karin bayani