Dan bindiga ya kashe mutane a Denver na Amurka

Motocin kai dauki a Denver Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Motocin kai dauki a Denver

'Yan sanda a Denver a Amurka, sun ce wani dan bindiga daya rufe fuskarsa, ya kashe mutane 12 tare da raunata mutane hamsin, a lokacin daya bude wuta a wani gidan kallon fim.

Da farko dai 'yan sanda sun bada rahoton kashe mutane 14 a cikin silman, lokacin ana kallon wani fim mai suna "The Dark Knight Rises".

Shaidu a Silman dake Aurora dake wajen birnin Denver, sun ce wani mutum kwatsam ya tsaya gaban magijin kallo, ya soma harbin kai mai uwa dawabi.

Babban jami'in 'yan sanda na Aurora, Daniel Oates, ya bayyana cewar da misalin karfe 12 da rabi na safiyar yau wani ya bayyana a gaban wajen kallo na Century 16, kafin ya soma karkashe mutane.

'Yan sanda sunce sun damke wanda ake zargin, wato James Holmes a wajen ajiye mutoci.

Karin bayani