BBC navigation

'Yan sanda sun shiga gidan James Holmes

An sabunta: 21 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 18:57 GMT
Yan sanda na kokarin shiga gidan James Holmes

Yan sanda na kokarin shiga gidan James Holmes

Kwararrun kan kunce bama bamai a jahar Colorado na kasar Amurka sun kunce wasu abubuwan fashewa da aka dana a gidan dan bindigar da ake zargi da kashe mutane 12 a wata Silima.

'Yan san da sun ce anyi nasarar fasa abubuwa da dama da aka dana a jikin wayoyi, kuma hakan zai sa su shiga cikin gidan laiya lau.

Wakiliyar BBC ta ce ya dauki kwarru kan kunce bama-bamai da ma'aikatan kashe gobara da 'yan sanda sama da sa'o'i talatin kafin su tsara yadda za'a iya shiga gidan lafiya.

Har yanzu 'yan sandan zasu kunce wasu karin abubuwan fashewar dake cikin gidan

Har yanzu ana tsare da mutumin da ake zargin James Holmes. An kamashi ne jim kadan da harin da ya kai Sinmar dake Denver ranar juma'a da daddare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.