An kashe mutane bakwai a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Ivory Coast, Bert Koenders, ya ce an kashe akalla mutane bakwai a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar.

Ya ce wasu mutane ne kimanin dari uku dauke da adduna da bindigogi suka kutsa kai cikin sansanin da ke kusa da garin Duku na yammacin kasar inda suka fara satar kayayyaki tare da kone matsugunan da aka kafa.

Hukumomin kasar Ivory Coast sun ce harin na ramuwar gayya ne bayan kisan da aka yi wa wadansu mutane hudu ranar Alhamis da daddare.

Mutane da dama sun tsere daga sansanin wanda ya kunshi kimanin mutane dubu biyar wadanda suka tsere wa rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2010.