Badakalar nukiliya a Japan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kokarin gyara a tashar Fukushima

Wani kamfanin gine-gine a kasar Japan dake kokarin gyara tashar makamashin nukiliya ta Fukushima wadda ta lalace, ya amsa cewa ya nemi ma'aikattan kamfanin da kada su bayyana ainahin yadda suke aiki a wajen da turirun nukiliya yake.

Shugaban kamfanin na Build Up, Takasha Wada ya tabbatar da cewa wani babban jami'i ya fadawa ma'aikatan su rufe injinan dake auna turirin nukiliyar dake fita.

Ya kuma fadawa ma'aikatan cewaa, in ba haka ba nan-da-nan zasu shigar da kara kuma ba zasu iya aiki ba. Kimanin ma'aikata tara ne suka yi hakan amma sauran sun ki yi kuma suka bar kamfanin.

Yanzu haka dai gwamnati na gudanar da bincike kan lamarin.