Amurka zata taikamawa Kenya murkushe al-Shabaab

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Rahotanni daga Amurka sun ce ma'aikatar tsaron kasar zata samawa Kenya kananan na'urorin binciken tsaro guda takwas, a matsayin wani bangare na taimakon sojin da zata ba kasashen gabashin Afirka dan ta taimaka musu murkushe 'yan gwagwarmayar Ismala na Al-Shabaab a Somalia.

Jaridar World Street ta ce Kenya zata samu na'urorin wadanda ba sa dauke da makamai amma za'ai amfani da su wajen gano wuraran da dakaru zasu kai hare hare ta sama ko ta kasa.

Jaridar ta ce na'urorin wani bangare ne wani shirin Amurka da zai kunshi manyan- motocin, da na'urorin sadarwa da bindigogin da za'a ba Burundi da Djibouti da kuma Uganda.

Karin bayani