Najeriya: an kai hari a jihar Kogi

Image caption Taswirar Najeriya

A Nigeria, rahotanni na nuna cewa, an kai hare haren bama bamai a wani ofishin yan sanda da wani banki dake yankin Iyara a jihar Kogi dake arewacin kasar.

Ya zuwa yanzu ba a ka iga tabbatar da adadin mutanen da suka rasu ba amma hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa a jihar ta tabbatar da rasuwar dan sanda guda yayin da wata kuma ta jikkakata.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Mr Simon Ile ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bada wani karin bayani ba.

A kwanakin bayanan nan wasu sassan jihar Kogin sun yi fama da hare-hare.