'An kashe mutane 200 a fadan Syria na baya bayan nan'

Image caption Wadansu mutane da aka kashe a Syria

'Yan adawa masu fafutuka a kasar Syria sun ce an kashe mutane sama da 200 a fadan baya-bayan da ake yi a kasar, mafi rinjayen su kuma a birnin Damascus.

Ranar Juma'a an bayar da rahotannin barkewar wani sabon fada a biranen Damascus da kuma Aleppo da ke arewacin kasar, inda a baya birni ne da gwamnati ke da iko da shi.

Masu fafutuka sun ce mutane arba'in aka kashe a Aleppo.

Gwamnatin kasar dai ta ce jami'an tsaro na yin nasara wajen murkushe 'yan ta'addan da suka shiga birnin Damascus.

An yi jana'izar surukin Assad

Gidan talabijin na Syria ya nuna hotunan jana'izar da aka yi wa surukin shugaba Assad, Assef Shawkat, da manyan jami'an tsaron kasar guda biyu, ciki har da Ministan Tsaro, wadanda aka kashe a wani harin bom da aka kai musu ranar Laraba.

An kwashe wasu sa'oi kafin a nuna jana'izar ta su wacce aka gudanar a wani yanki mai cike da tsaunuka da ke arewa-maso- kudancin birnin Damascus.

A cewar masu fafutuka, daga yankin ne dakarun gwamnati suka rika harba manyan makamai zuwa wuraren da 'yan tawaye suka fi karfi.

Mutum na hudu cikin manyan jami'an gwammatin da aka kai wa harin ya mutu ranar Juma'a sakamakon raunukan da ya samu.

Kungiyar Muslim Brotherhoood, wacce ita ce kungiya mafi girma a kasar, ta ce iko na cigaba da kubucewa gwamnatin Assad a sassa daban daban na kasar.

A cewarta, shi yasa ma ya kamata kowanne dan kasar ya tattabar ya bi doka don a samu zaman lafiya.

Karin bayani