Bauchi: an kai harin bam

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani harin bam a Najeriya

Rahotanni daga Jihar Bauchi a Nijeriya na cewa wani bam ya tashi a unguwar da ake kira Bayan Gari inda mutum guda ya rasa ransa wasu da dama kuma suka jikkata.

Bayanan da na samu dai na cewa wannan bam ya tashi ne a garin na Bauchi da misalign karfe shida na yammacin yau a unguwar da ake kira Bayan Gari, ko kuma Tudun Wadan Dan Iya inda mazauna unguwar da kewaye suka bada labarin jin wata kara mai karfin gaske.

Hukumomin tsaro dai sun tabbatar da faruwar lamarin suna amsu cewa suna kan bincike.

Jihar ta Bauchi na daya daga cikin jihohin Nijeriya masu yawan fama da hare-haren bama-bama a ci gaba da matsalar tabarbarewar tsaro da kasar ke fuskanta.