Kaucewa biyan haraji na karuwa

Wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa hamshakan masu kudi na duniya na rike da akalla dala triliyan ashirin da daya a tudun mun tsira na kin biyan haraji.

Kuma wannan adadin ya kai kudadan shigar jama'a a kasashen Amurka da Japan idan aka hadasu wuri guda.

Rahotan ya ce asarar harajin da wadannan mutanen ke janyowa ga tattalin arzikin duniya na da girman gaske kuma zai matukar kawo sauyi ga kasashe da dama masu tasowa.

Rahotan wanda wata kungiya mai suna Tax Justice Network ta fitar ya ce, bankuna uku masu zaman kansu dake ajiyewa hamshakan masu kudi na duniya kadarorinsu su ne bankin UBS da bankin Credit Suisse da kuma Goldman Sachs.