Jigon 'yan adawar Cuba ya mutu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jigogi 'yan adawar Cuba

Daya daga cikin fitattun 'yan adawa a kasar Cuba Oswalda Paya ya mutu a cikin wani hadarin mota ranar lahadi.

Paya wanda shine jagoran kungiyar masu adawa da gwamnatin kwaminisanci ta kasar Cuba ta Christian Liberation movement ya mutu ne yana da shekaru sittin.

Hadarin dai ya faru ne lokacinda Oswaldo Paya ke kan wata tafiya zuwa Lardin Granma na gabashin kasar.

Babu dai cikkakun bayanai kan yadda hadarin ya afku amma wani takwaransa dan adawa Yoani Sanchez mai saka bayanai a shafin internet yace limamin darkar katolika na lardin Granma Carlos Amanda ne ya tabbatarda mutuwar Mr. Paya; sai dai babu wani bayani da aka samu ya zuwa yanzu daga iyalansa dangane da mutuwar ta sa.

Ficensa a duniya

Mr. Paya dai ya fara yin fice ne a idon duniya sa'adda ya jagoranci wani kamfe na kiran da a yi wata kuri'ar raba gardama kan ko kasar ta cigaba da kasancewa kan mulkin jam'iyya daya da ko kuma a'a inda ya samu mutane dubu talatin suka mara masa baya ta hanyar saka hannu kan wannan bukatar tasa.

Ko da yake dai gwamnatin kasar ta Fidel Castro tayi fatali da bukatar tasa a zaman wata makarkashiya daga Amurka tayi wa mulkinsa na shekaru arbai'n zagon kasa, hakan ya sanya Paya yayi fice a zama jagoran neman sauyin dimokradiyya cikin ruwan sanyi a kasar Cuba mai biyar tsarin gurguzu.

A shekara ta 2002 an bashi babbar lambar yabo da tarayyar turai ke baiwa wanda yayi fice a fafutukar kare hakkin dan adam da ake kira Sakharov Prize.

An tasa keyar Oswaldo Paya wanda rkakken da darikar katolika ne zuwa sansanin aikin karfi bisa dalilan addini a shekarun alif da dari tara da sittin, kuma ya jure razanarwa da kuma cin-zarafi sau da yawa wajen kafa kungiyar y'an adawa ta farko a Cuba wadda ta game kasar baki daya.

Mabiyansa arba'in ciki har da mataimakansa na kud-da-kud na daga cikin masu sukar shugaba Castro su sabain da biyar da aka kama a shekara ta 2003 kuma aka yanke musu hukumcin daurin shekaru 28 a kurkuku kodayake an sako su a shekarar bara.

Paya wanda mutum ne mai taushin murya kuma Injiniyan na'urorin asibiti da baya da fankama, ya cigaba da kiran yin taron kasa tsakanin al'ummar Cuba da 'yan jam'iyyar kwaminis mai mulki domin tattauna yadda za a mayarda kasar kan tsarin dimokradiyya cikin ruwan sanyi har zuwa lokacin mutuwar tasa.

Karin bayani