An kashe mutane sama da dari a Iraki

Hare-haren bam a Iraki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-haren bam a Iraki

Mutane sama da dari ne suka mutu a sakamakon hare hare a wurare daban daban, galibi a kan jami'an tsaro a sassa daban daban na kasar Iraki.

Wasu mutanen sama da dari biyu sun jikkata.

Hare haren na yau sun kasance daya daga cikin mafiya muni tun bayan janyewar dakarun Amurka daga kasar.

An rika tayar da bama bamai cikin kananan motoci, da kuma manyan bindigogin iggwa wajen kai hare haren.

A daya daga cikin hare haren an kashe sojoji goma sha biyar a lardin Salaheddin.

Wani wanda aka kai harin a gabansa a Kirkuk ya ce rashin samar da tsaro ga mutane shi ke janyo kai irin wadannan hare-hare dake sanadiyyar rasa rayukan al'umma.

Ko a jiya wasu jerin hare haren bama baman a sassa daban daban na Irakin sun kashe mutane akalla sha bakwai, suka kuma raunata wasu da dama

Karin bayani