Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 40 a jos

Ambaliyar ruwa a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwa a Najeriya

Ana cigaba da ayyukan ceto a Jos babban birnin jihar Plateau, sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku.

Kawo yanzu an gano gawawwakin mutane kusan 40 da suka mutu a sanadiyar ambaliyar ruwan.

Kungiyar agajin gaggawa ta Red Cross ta ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka bata ba.

A jiya ne aka kwana ana sheka ruwan sama a garin jos, abin da ya janyo ambaliyar ruwan da ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.

Najeriya ta dade tana fuskantar matsalar ambaliyar ruwa da kan janyo asarar rayuka da dukiyoyi.