Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane kusan 40 a Jos

Ambaliyar ruwa a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwa a Najeriya

Rahotanni daga Jos, babban birnin Jihar Filato a Nijeriya, sun ce mutane kimanin arba’in sun rasa rayukansu wadansu da dama kuma sun bata sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a wadansu unguwanni bayan ruwan saman da aka yini aka kuma kusan kwana ana yi.

Cikin wadanda suka mutu dai har da wata dattijuwa mai kimanin shekaru casa’in da kuma wata jiririya mai kimanin watanni uku da haihuwa.

Unguwannin da ambaliyar ta fi shafa dai su ne Gangare, da Unguwar Rogo, da Tudun OC, da Rikkos, bayan da aka shafe sa’o’i da dama ana ruwan sama kamar da bakin kwarya ranar Lahadi, kuma akasarin wuraren da al’amarin ya shafa a kusa da rafi suke.

Ambaliyar dai ta sha kan gidaje da dama— wadansunsu sun ruguje baki daya, kuma mutane kimanin arba’in sun mutu, yayinda wadansu kimanin haka suka salwanta.

Ruwan mai toroko ya kuma yi awon gaba da dukiya mai dimbin yawa.

Ambaliyar ta ci shida daga cikin ’ya’ya takwas na wata mata mai suna Malama Indo, har da jaririya ’yar watanni uku.

“Na dauki [jakunkunan] Ghana-Must-Go na sassaka a kan gado, kafin in koma in dauki yaran kawai sai dakin ya fadi.... Maigidana ya koma ya dauki yaran sai bai gansu ba sai wannan guda dayan, duk sun bi ruwa”, inji Malama Indo.

Ta kuma kara da cewa: “Allah Shi ya san yadda zai yi da ni; ba abin da zan ce sai dai in yi hamdala ga Uban Giji, Allah Ya ba ni dangana, su kuma Allah Ya jikansu Ya gafarta masu”.

Ma’aikatan agaji na hukumomin gwamnati da na addini da masu zaman kansu na ci gaba da aikin ceto da nufin gano gawarwaki da wadanda suka bata.

A cewar Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross a jihar Filato, Mista Manasseh Pampe, gawarwakin da aka gano ya zuwa yanzu sun kai talatin da biyar.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya, wato NEMA, ta ce tana kan tattara alkaluman wadanda suka rasa muhallansu da nufin taimaka masu.