Amurka ta yi gargadi game da makaman kare dangin Syria

tankokin yakin Syria
Image caption tankokin yakin Syria

Amurka ta gargadin gwamnatin Syria kada ta yi amfani da makamai masu guba, bayan da kasar ta Syria ta nuna alamun cewar za ta yi amfani dasu idan har dakarun kasashen waje suka kai mata hari.

Wannan gargadin na zuwa ne, bayan da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Syria a karon farko, ya tabbatar da cewar kasar ta mallaki makamai masu guba. Shugaban Rasha, Vladmir Putin ya ce ta hanyar sasantawa kawai ya kamata a warware tashin hankalin na Syria.

Wakilin BBC a gabas ta tsakiya, ya ce babbar damuwar da ake da ita, shine idan gwamnatin ta kife, kada makamai masu guban su shiga hannun masu tsatsauran ra'ayin musulunci.

A daya bangaren, kuma kungiyoyin agaji sun ce an samu karuwa ta mutanen dake bukatar agajin gaggawa a ciki da wajen kasar ta Syria, sakamaon tashin hankalin da ya kara ta'azzara.

Kungiyar agaji Red Crescent a Syria ta kiyasta cewa akwai mutane miliyan daya da rabi da suka suka rasa muhallansu a cikin Syria, kuma adadinsu na karuwa.

Karin bayani